Rayuwar Sayyadina Ali Da Ayyukansa Na Yada Addinin Musulunci (VII)

https://celebritycontent.com/2020/02/18/rayuwar-sayyadina-ali-da-ayyukansa-na-yada-addinin-musulunci-vii/

Cigaba daga inda mu ka tsaya a makon da ya gabata.

Mutanen kufa kuwa sun amsa wannan kira na Sarkin Musulmai domin sama da mutane dubu goma sha biyu ne suka fita don mara masa baya.

Ammar ya ci gaba da bayar da goyon bayansa ga Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam har ajalinsa ya cim masa a hannun daya daga cikin mutanen Mu’awiyah. Babu shakka kuwa mutuwarsa ta sa Mu’awiyah da jama’arsa cikin bala’I da masifa. Domin kuwa da yawansu (musamman ma dai Sahabbai daga cikinsu) sun canza sheka daga wajen Mu’awiyah suka koma bangaren Sayyadina Ali saboda la’akari da wani sanannen hadisi a tsakaninsu wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yake cewa, Ammar zai gamu da ajalinsa a hannun wata kungiya mai kira izuwa ga wutar jahannama. (Sahihul Bukhari littafin Sallah, Babin taimako a Masallaci Hadisi na 447).

Ra’ayin Sahabbai Dangane Da Wannan Yaki:

Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sun kasu kashi uku dangane da wannan yakin.

Kashi na farko su ne wadanda su ke da ra’ayin cewa, yakin bai ma dace ba gaba daya. Kuma kan al’umma ya wajaba ya hadu a wuri daya maimakon yaki a tsakanin junansu. Irin wadannan bayin Allan sun yarda da khalifancin Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam kuma sun yi masa mubaya’a, amma dai yakin ne ba su aminta da aukuwarsa ba. Wadannan su ne akasarin Sahabbai, a cikinsu har da Sa’adu Dan Abu Wakkas da Muhammadu Dan Maslamah da Abdullahi Dan Umar bin Khattabi da Abu Musa al Ash’ari (Gwamnan Kufa) da Abu Bakrata Al Thakafi da Abu Mas’ud al Ansari da makamantansu. Hujjojin wadannan bayin Allan suna da dama, kuma sun hada da duk hadissan da ke magana a kan barin yaki lokacin fitina. A cikinsu ma har da wadanda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi alkawari da su cewa, duk halin da aka shiga kar su yi yaki da Musulmai. (Sahihul Bukhari kitabul Fitan (8/95), da Sunan Al Tirmizi Kitabul fitan (3/332), da kuma Musnad na Ahmad (4/225))

Kashi na biyu kuwa, suna ganin cewa, tun da ya ke Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam shi ne nadadden Sarkin Musulmai, wanda ya wajaba a yi wa biyayya, wajibi ne a yaki dukkan wanda ya fandare masa. A kan haka suna yaki tare da shi a kan Mu’awiyah da jama’arsa. Suna kuma kafa hujja da dalillai na Alkur’ani da hadisi masu nuna wajabcin biyayya ga shugabanni.

Daga cikin wadanda suka dauki wannan matsayin har da fitattun Sahabbai irin su Abdullahi Dan Abbas da Ash’as Dan Kais da Ammaru Dan Yasir da Maliku Dan Ka’abu Al Hamdani da dai sauransu. Ga wata tattaunawa da ta gudana a tsakanin Ammaru da Abu Mas’ud Al Ansari Radiyallahu Anhuma (daga cikin masu ra’ayin farko na kauracewa yakin) a kan wannan mabanbancin ra’ayin nasu, Buhari ya ruwaito ta kamar haka:

Abu Mas’ud ya ce. “Ya kai Ammar! Ka sani duk a cikin tsaranka babu wanda ya kai matsayinka a wurina. Kuma ba ka taba sanya kanka a cikin wani lamari ba wanda yake aibanta ka a wurina sai gaggawar da kake yi a cikin wannan fitina.

Ammaru ya ce dashi. “Ya kai Baban Mas’ud! Ni kuma wallahi ba ka da wani aibi a gurina kai da abokinka (Amru Dan Ass) wanda yake aibata ku tun bayan rasuwar Manzon Allah kamar janye jikinku daga wannan lamari (yana nufin taimaka wa Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam).

A yayin da kashi na uku na Sahabbai su ko su ke ganin cewa, Mu’awiyah ne yake da hakkin ya nemi fansar jinin dan uwansa Khalifa Sayyadina Usman Radiyallahu Anhu, kuma dole ne a taimaka masa don ya cimma biyan wannan bukata. Suna kafa hujja da ayar Suratul Isra’i wadda Allah a cikinta yake cewa.

“Wanda duk aka kashe shi a kan zalunci to, hakika mun sanya hujja ga waliyyinsa (a kan ya nemi fansa), sai dai kar ya wuce iyaka a wajen kisan (ramuwa), domin lalle shi abin taimakawa ne.” (Suratul Isra’i, Aya ta 33).

Haka kuma suna kafa hujja da hadissan da suka bayyana cewa, fitina zata auku, kuma idan ta auku Usman shi yake a kan gaskiya tare da mutanensa. Sai suna ganin su ne mutanen Usman tun da su ke fada dominsa.

Daga cikin masu wannan ra’ayi akwai Sahabbai kamar Amru Dan Ass da Ubadata Dan Samitu da Abud Darda’I da Abu Umamata Al Bahili da Amru Dan Ambasata da dai sauransu.

Idan muka yi la’akari da hadisin da Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya ruwaito daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa. “A yi bushara ga duk wanda ya kashe Zubairu da wuta.” Da hadisin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ma Dalhah bushara da zai yi shahada za mu gane cewa, wadansu suna da uzuri a yakar Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam da suka yi. Domin kuwa dama ba shi suka zo yaka ba.

Mu’awiyah yaki ya yiwa Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam mubaya’a, saboda wai sai an ba shi makasan Sayyadina Usman Radiyallahu Anhu ya kashe saboda hakinsa ne, domin shi dan uwan Sayyadina Usmanu ne. Shi kuma Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam na cewa, in kana son haka, ka amince da shugabancin da aka nada tukuna, sai ka kawo kara ga gwamnati ta bincika tayi hukunci. Mu’awiyah na nan a kan bakarsa, ni ba zan yi ma ka mubaya’ah ba in dai har ba za ka iya daukar fansar wanda ya gabace ka ba, kuma ba za ka ba ni dama ni da ni ke da hakki ba. (Mukaddima, na Dan Khludun (1/257)).

Wafatin Sayyadina Ali:

Bayan yarjejeniyar yaudara da aka yi a yakin Siffin, abin da ake kira Tahkim, tsakanin Amru Dan Ass da Abu Musa Al’Ash’ari Radiyallahu Anhu, sai wasu kungiya daga cikin Musulmai suka fandare wa Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam, wanda ake kiransu Khawarijawa, duk da cewa Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya yi kokarin nusantar da su kan wannan tafarki da suka dauka, da kuma basu lokaci ko sa tuba, amma dai sun ki yin haka, sai ma dai tara sojoji suke don yakansa da kuma halalta jininsa, abin da ya haifar da yaki a tsakaninsu. Yakin da ake kira da Yakin Naharawan. To bayan wannan yaki da kuma nasarar da dakarun gaskiya karkashin jagorancin Sayyadina Ali Dan Abu Dalib Alaihi Salatu Wasallam suka samu akan Khawarijawan. (Hadissan falalar yakar khawarij a cikin Sahihul Bukhari, Kitabul Fitan, Babu Katlil Khawarij).

Khawarijawa dai sun shirya wata makarkashiya wadda ke da nufin kawo karshen Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam da Mu’awiyah da Amru Dan Ass baki daya, wadanda su ne dagutai na wannan zamani a cewarsu. Sun kuma shata rana da lokacin da za su gudanar da wannan danyen aiki. Ranar kuwa ita ce, ranar 17 ga Ramadan, shekara ta Arba’in bayan hijira a dai-dai lokacin da kowanensu yake fitowa sallar asubahi.

Bisa ga haka ne, Abdul Rahman Dan Muljam ya tasar ma Kufa, mazaunin Sayyiduna Ali Alaihi Salatu Wasallam. Al Barak Dan Abdullahi shi kuma ya je Sham, mazaunin Mu’awiyah, yayin da Amru Dan Bakr Al Tamimi zai tasar ma wajen Amru Dan Ass. Da lokaci ya yi, kowannensu ya zartar da abin da a ka dora ma sa.

Bisa ga haka ne, Abdul Rahman Dan Muljam ya tasar ma Kufa, mazaunin Sayyiduna Ali Alaihi Salatu Wasallam. Al Barak Dan Abdullahi shi kuma ya je Sham, mazaunin Mu’awiyah, yayin da Amru Dan Bakr Al Tamimi zai tasar ma wajen Amru Dan Ass. Da lokaci ya yi, kowannensu ya zartas da abin da aka dora masa.

Shi dai Al Barak da yaje wajen Mu’awiyah, bai samu sa’arsa ba, saboda an gano shi tun bai kammala mugun aikin ba. Sai dai ya ji wa Mu’awiyah rauni a cinya, wadda ya yi kwanuka ya na jinyar ta. A kan wannan dalili Mu’awiyah ya nemi matsara a karon farko a tarihin. Shi ma dai Amru kwanansa ya na gaba, domin a ranar da aka shirya yin wannan ta’asar a kansa bai fito sallar ba. To, da ya ke cikin duhun asubahi ne, dan sakon Khawariawaj sai ya kashe limamin da ya bayar da Sallah a rannan, zaton sa cewa, gwamnan ne da kansa. Don haka Na’ibi wanda kuma shi ne kwamandan ‘yan sanda, Kharijah dan Huzafa ya yi shahada a madadin mai gidansa.

Za mu dakata anan, sai mako mai zuwa In sha Allahu za mu kawo muku karshen tarihin wannan babban gwarzon musulunci.

Bayan haka, mu na sanar da ’yan uwa abota wannan tarihin cewa, da yarda Allah za mu fara kawo mu ku tarihin iyayyen muminai matan Manzon Allah (SAW) a irin wannan rana ta Littinin a wannan jaridar ta LEADERSHIP A YAU mai albarka daga makon gobe bisa izinin Allah.

Mu na rokon Ubangiji Allah ya albarka wannan aikin namu, ya sa ya amfani al’ummar Annabi (SAW) bakidaya.

Daga dan uwanku, Mohammed Bala Garba, Maiduguri, 08098331260.

This content was originally published here.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *